Kamaru ta yi canjaras da Jamus 2-2

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Samuel Etoo ne ya fara jefa kwallo a ragar Jamus

Jamus ta yi canjaras da Kamaru 2-2 a wasan sada zumunta na shirin zuwa gasar Kofin Duniya.

Wasan da aka yi a Borussia-Park da ke Jamus Samuel Eto ne ya fara sa kwallo a ragar Jamus a minti na 62, sai Muller ya rama a minti na 66.

Jamus ta kara kwallo ta biyu a minti na 71 ta hannun Schurrle amma kuma Choupo-Moting ya rama wa Kamarun minti bakwai tsakani.

Sauran wasannin da aka yi ranar Lahadi

Panama 1 - 1 Serbia ; Amurka 2 - 1 Turkiyya

Sweden 0 - 2 Belgium ; Fransa 1 - 1 Paraguay