David Villa zai bar Atletico Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption David Villa mai shekaru 32 ya ce ya samu gayyatar da ba zai iya watsi da ita ba daga wata kungiya da bai bayyana sunanta ba.

Dan wasan da ya fi cin kwallo a tarihi a Spain David Villa zai bar Atletico Madrid bayan shekara daya da zakarun La Ligan.

Dan wasan na gaba yana cikin tawagar 'yan wasan Spain 23 ta gasar Kofin Duniya.

Ana dai jita-jitar cewa zai koma kungiyar New York City FC ta Amurka wadda kuma mallakar Manchester City ce.

Villa ya ci kwallaye 13 a La Liga abin da ya taimaka wa Atletico Madrid ta doke Barcelona da Real Madrid ta dauki kofin a karon farko tun 1996.

Sau 94 yana buga wa Spain wasa inda ya ci musu kwallaye 56, ya taimaka suka dauki kofin Turai a 2008 da na duniya a 2010.

Sai dai bai samu damar zuwa gasar Kofin kasashen Turan ba a 2012 saboda karayar da ya yi a kafa.

David Villa ya ce, ''yana matukar godiya ga mutanen Atletico da wadanda suka yi kokarin shawo kansa ya tsaya, kamar kocinsu Diego Simeone da mataimakansa.