Moyes: 'ba a ba ni lokaci ba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Bayan na tafi Rooney da Fletcher sun bayyana goyon bayansu gare ni'

Tsohon kocin Manchester United David Moyes ya ce abin takaici ne ba a ba shi karin lokaci ba a Old Trafford.

Amma ya ce ya karu da ilimi daga aikin watanni goma da ya yi da kungiyar, kuma ya ce Sir Alex Ferguson ya mara masa baya a dan lokacin da ya yi a klub din.

Kocin ya ce ya yi tsammanin za a ba shi karin lokaci domin ya aiwatar da gagarumin sauyi a kungiyar.

Moyes mai shekaru 51wanda ya ce ya ji dadin zamansa a United ya ce yana duba bukatarsa da wasu kungiyoyin ke yi a yanzu.

A ranar goma ga watan Afrilu Man United ta kori David Moyes wanda ya gaji Sir Alex Ferguson wata goma bayan ya fara kwatiragin shekaru shida.

Karin bayani