Qatar 2022:Za a gana a kan cin hanci

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A na zargin wasu jami'an fifa sun karbi na goro don su amince qatar ta dauki nauyin gasar a shekarar 2022

Masu ruwa da tsaki kan shirya gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022, za su gana da mai bincike daga Fifa Micheal Garcia ranar litinin, don tattaunawa kan kiraye-kirayen da ake na hana kasar daukar nauyin gasar.

Jaridar Sunday Times ta ruwaito cewa an bai wa jami'an hukumar fifa toshiyar baki na miliyoyin daloli ga wadanda suka ba da goyon baya Qatar ta dauki nauyin gasar.

Sai dai mataimakin shugaban hukumar ta fifa Jim Boyce ya ce a shirye yake ya amince a sake kada kuri'a matukar zargin da ake ya tabbata.

Amma kwamatin shirya gasar na Qatar ya musanta zargin da ake masa na rashin gaskiya.

Garcia, wanda lauya ne a Amurka, da ke dab da ganawa da mahukuntan Qatar a Oman, tuni ya fara gudanar da bincike a kan tayin shirya gasar cin kofin duniya ta shekarar 2018 da 2022.

Sunday Times ta ce ana zargin jami'an na Fifa da karbar fam miliyan uku a matsayin toshiyar baki don su amince Qatar ta dauki nauyin gasar a shekarar 2022.