'Yan wasan Ingila za su rika taken kasar

Image caption Kungiyar ta Hodgson ta buga wasannin sada zumunta biyu cikin makon da ya gabata a kasar Amurka.

Kocin Ingila Roy Hodgson ya ce akwai bukatar 'yan wasansa su rika yin alfahari da kasar da suke wakilta ta hanyar rera taken kasar a gasar cin kofin duniya.

Hodgson yana son 'yan wasan su nuna kishi a duk lokacin da aka kunna waka mai taken "God Save The Queen" a wasannin da za ayi a Brazil.

Hodgson, mai shekaru 66, ya ce "da wahala ka yi wasa da abokan hamayya sai ka ga 'yan wasan sun dora hannu kan kirji suna rera taken kasar su kowa na ji gwargwadon iko."

Ya ce: "tun da wuri muka yanke hukuncin bin sahun sauran kungiyoyin kwallon kafa na duniya."

Kulob din na Ingila ya isa Miami ranar Lahadi a ci gaba da shiye-shiryen tinkarar gasar cin kofin duniya inda a wasan bude gasar, Ingila za ta kara da Manaus ranar 14 ga watan Yuli.