Lambert ya koma Liverpool kan £4m

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption "Mahaifana sun yi kukan dadi lokacin da suka ji wannan kyakkyawan labari"'.

Dan wasan gaba na Southampton Rickie Lambert ya koma Liverpool kan kudi fam 4m.

Dan wasan, mai shekaru 32, na cikin tawagar 'yan kwallon Ingila da za su buga gasar cin kofin duniya da za a yi a Brazil a wannan wata.

An yi wa Lambert gwajin lafiya ne lokacin da yake buga wa kasar wasan sada zumunci, kuma ana kyautata zaton ya rattaba hannu domin yin shekara biyu a kungiyar.

An haife shi ne a Liverpool kuma ya kwashe shekaru biyar yana taka leda a Anfield a matsayin ''matashin dan wasa''.

Karin bayani