Lampard zai bar Chelsea

Image caption Lampard dan tsohon dan wasan baya na West Ham Frank Lampard babba ya fara yi wa Ingila wasa a 1999.

Frank Lampard ya sanar cewa zai bar Chelsea bayan shekaru 13 a Stamford Bridge amma bai bayyana inda zai koma ba.

Dan wasan na Ingila mai shekaru 35 wanda ya fi kowa ne dan wasa a tarihin kungiyar cin kwallo, har 211 ba wani kwantiragi a kansa yanzu.

Tun da ya koma Chelsea daga West Ham a 2011, Lampard ya dauki manyan kofuna 11 da suka hada da Premier uku da na Zakarun Turai a 2012.

A halin yanzu dai lampard din yana cikin tawagar Ingila da ta tafi Miami kafin gasar cin Kofin Duniya.

Har yanzu bai sanar ko zai yi ritaya ba kuma kungiyoyi 16 sun neme shi, amma sai bayan gasar kofin duniya zai bayyana matsayinsa.

Haka shi ma Ashley Cole mai shekaru 33 ba wani kwantiragi a kansa kuma zai bar Chelsea bayan shekaru 8.

Karin bayani