Rukunin D

Uruguay:

Hakkin mallakar hoto AP

Kasar Uruguay ce ta soma lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1930 kuma a shekarun baya ta haskaka.

Kocin tawagar 'yan kwallon kasar Oscar Tabarez na kokarin taka rawar gani saboda a nahiyarsu ake wannan gasar kuma ya jagoranci kasar ta lashe gasar Copa America.

Uruguay za ta sa'ido kan Luis Suarez, Edinson Cavani da kuma Diego Forlan su kai ta gaci.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Fernando Muslera (Galatasaray), Martin Silva (Vasco da Gama), Rodrigo Munoz (Libertad).

'Yan wasan baya: Maximiliano Pereira (Benfica), Diego Lugano (West Bromwich Albion), Diego Godin, Jose Maria Gimenez (both Atletico Madrid), Sebastian Coates (Liverpool), Martin Caceres (Juventus), Jorge Fucile (Porto).

'Yan wasan tsakiya: Alvaro Gonzalez (Lazio), Alvaro Pereira (Sao Paulo), Walter Gargano (Parma), Egidio Arevalo Rios (Morelia), Diego Perez (Bologna), Cristian Rodriguez (Atletico Madrid), Gaston Ramirez (Southampton), Nicolas Lodeiro (Botafogo).

'Yan wasan gaba: Luis Suarez (Liverpool), Edinson Cavani (Paris St-Germain), Abel Hernandez (Palermo), Diego Forlan (Cerezo Osaka), Christian Stuani (Espanyol).

Costa Rica:

Hakkin mallakar hoto AP

A iya cewa wannan ce tawaga mafi karfi da kasar Costa Rica ta kai zuwa gasar cin kofin duniya amma kuma kasar ba ta yi sa'an rukuni ba.

Costa Rica ta kasance ta biyu a yankin Arewacin Amurka inda ta samu nasara a wasanni biyar da ta buga a gida.

Kocin kasar Jorge Luis Pinto wanda dan kasar Colombia ne, zai yi fatan cewar golansa Keylor Navas ya kasance kan ganiyarsa don haskakawa a gasar.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Keylor Navas (Levante), Patrick Pemberton (Alajuelense) Daniel Cambronero (Herediano).

'Yan wasan baya: Johnny Acosta (Alajuelense), Giancarlo Gonzalez (Columbus Crew), Michael Umana (Saprissa), Oscar Duarte (Bruges), Waylon Francis (Columbus Crew), Heiner Mora (Saprissa), Junior Diaz (Mainz 05), Christian Gamboa (Rosenborg), Roy Miller (New York Red Bulls).

'Yan wasan tsakiya: Celso Borges (AIK), Christian Bolanos (Copenhagen), Esteban Granados (Herediano), Michael Barrantes (Aalesund), Yeltsin Tejeda (Saprissa), Diego Calvo (Valerenga), Jose Miguel Cubero (Herediano).

'Yan wasan gaba: Bryan Ruiz (PSV Eindhoven, on loan from Fulham), Joel Campbell (Olympiakos, on loan from Arsenal), Randall Brenes (Cartagines), Marco Urena (FC Kuban Krasnodar).

Ingila:

Hakkin mallakar hoto AFP

Tawagar Ingila ta tsallake zuwa gasar cin kofin duniya ba tare da wata kasa ta doke ta a rukuninta ba, kuma kwallaye hudu kawai aka zurawa kasar a wasannin share fage.

Kocin kasar Roy Hodgson, zai kasance dan Ingila na farko da zai jagoranci kasar zuwa gasar cin kofin duniya a karon farko cikin shekaru 16.

'Yan wasa kamarsu Wayne Rooney da Steven Gerrard da kuma Daniel Strurridge ake saran za su fitar da kasar daga jin kunya.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Fraser Forster (Celtic), Ben Foster (West Bromwich Albion), Joe Hart (Manchester City).

'Yan wasan baya: Leighton Baines (Everton), Gary Cahill (Chelsea), Phil Jagielka (Everton), Glen Johnson (Liverpool), Phil Jones (Manchester United), Luke Shaw (Southampton), Chris Smalling (Manchester United).

'Yan wasan tsakiya: Ross Barkley (Everton), Steven Gerrard, Jordan Henderson (both Liverpool), Adam Lallana (Southampton), Frank Lampard (Chelsea), James Milner (Manchester City), Alex Oxlade-Chamberlain (Arsenal), Raheem Sterling (Liverpool), Jack Wilshere (Arsenal).

'Yan wasan gaba: Rickie Lambert (Southampton), Wayne Rooney (Manchester United), Daniel Sturridge (Liverpool), Danny Welbeck (Manchester United)

Italiya:

Hakkin mallakar hoto Reuters

Tawagar kasar Italiya ta tsallake zuwa wannan gasar tun ana sauran wasanni biyu a kamalla wasannin share fage na rukunin da take.

Italiya wacce ta lashe gasar kofin duniya sau hudu a baya (1934, 1938, 1982 and 2006) a wannan karon Cesare Prandelli ne zai jagoranci kasar.

'Yan wasa kamarsu Mario Balotelli da Andre Pirlo sune ake saran za su hasakaka a lokacin gasar.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Gianluigi Buffon (Juventus), Salvatore Sirigu (Paris St-Germain), Mattia Perin (Genoa).

'Yan wasan baya: Andrea Barzagli, Leonardo Bonucci, Giorigo Chiellini (all Juventus), Gabriel Paletta (Parma), Ignazio Abate, Mattia De Sciglio (both AC Milan), Matteo Darmian (Torino).

'Yan wasan tsakiya: Andrea Pirlo, Claudio Marchisio (both Juventus), Thiago Motta, Marco Verratti (both Paris St-Germain), Daniele De Rossi (AS Roma), Antonio Candreva (Lazio), Marco Parolo (Parma), Alberto Aquilani (Fiorentina).

'Yan wasan gaba: Mario Balotelli (AC Milan), Antonio Cassano (Parma), Alessio Cerci (Torino), Ciro Immobile (Torino), Lorenzo Insigne (Napoli).