Rukunin E

Switzerland:

Hakkin mallakar hoto AP

Kasar Switzerland na cike da matasan 'yan kwallo majiya karfi wadanda take saran kamar yadda suka haskaka lokacin wasannin share fage, za su iya kara bada mamaki a lokacin wannan gasar.

Tawagar karkashin jagorancin Ottmar Hitzfeld wacce ke buga salon wasa 4-3-2-1 za ta nemi kafa tarihi, saboda kasar ba ta taba wuce zagayen gabda na kusada karshe ba a tarihin gasar cin kofin duniya.

'Yan wasa kamar su Granit Xhaka da Xherdan Shaqiri ana kallonsu a matsayin madubi ga tawagar 'yan kwallon Switzerland.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Diego Benaglio (Wolfsburg), Roman Buerki (Grasshopper), Yann Sommer (Basel).

'Yan wasan baya: Johan Djourou (Hamburg), Michael Lang (Grasshopper), Stephan Lichtsteiner (Juventus), Ricardo Rodriguez (Wolfsburg), Fabian Schaer (Basel), Philippe Senderos (Valencia), Steve von Bergen (Young Boys), Reto Ziegler (Sassuolo).

'Yan wasan tsakiya: Tranquillo Barnetta (Eintracht Frankfurt), Valon Behrami (Napoli), Blerim Dzemaili (Napoli), Gelson Fernandes (Freiburg), Gokhan Inler (Napoli), Xherdan Shaqiri (Bayern Munich), Valentin Stocker (Basel).

'Yan wasan gaba: Josip Drmic (Nuremberg), Mario Gavranovic (Zurich), Admir Mehmedi (Freiburg), Haris Seferovic (Real Sociedad), Granit Xhaka (Borussia Monchengladbach).

Ecuador:

Hakkin mallakar hoto AP

Babu shakka kasar Ecuador na da gogaggun 'yan kwallo musamman masu tsare baya wadanda suka taimaka mata ta samu gurbin shiga wannan gasar.

Kasar ba ta taba wuce zagaye na biyu ba a gasar cin kofin duniya, kuma a halin yankin Kudancin Amurka, kasar ta haskaka karkashin jagorancin Reinaldo Rueda.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Maximo Banguera (Barcelona SC), Alexander Dominguez (LDU Quito), Adrian Bone (El Nacional).

'Yan wasa baya: Frickson Erazo (Flamengo), Jorge Guagua, Oscar Bagui, Gabriel Achilier (all Emelec), Walter Ayovi (Pachuca), Juan Carlos Paredes (Barcelona SC).

'Yan wasan tsakiya: Segundo Castillo (Al-Hilal), Carlos Gruezo (Stuttgart), Renato Ibarra (Vitesse Arnhem), Cristian Noboa (Dynamo Moscow), Luis Saritama (Barcelona SC), Antonio Valencia (Manchester United), Edison Mendez (Independiente Santa Fe), Fidel Martinez (Tijuana), Michael Arroyo (Atlante).

'Yan wasan gaba: Felipe Caicedo (Al-Jazira), Jefferson Montero (Morelia), Joao Rojas (Cruz Azul), Jaime Ayovi (Tijuana), Enner Valencia (Pachuca).

Faransa:

Hakkin mallakar hoto AFP

Faransa ta samu gurbin zuwa wannan gasar ne bayan nasaratta a kan Ukraine a wasan kifa daya kwala.

Kasar wacce ta lashe gasar cin kofin duniya a shekarar 1998, a bana kocinta Didier Deschamps zai yi fatan ya lashe gasar kamar yadda ya daga kofi a matsayinsa na kyaftin din tawagar.

'Yan wasa kamar su Paul Pogba da Franck Ribery wadanda suka taimaka kasar ta samu wannan gurbin, su ne ake saran su fitar da ita daga fuskantar raini

Tawaga:

Masu tsaron gida: Hugo Lloris (Tottenham Hotspur), Stephane Ruffier (Marseille), Mickael Landreau (Bastia).

'Yan wasan baya: Mathieu Debuchy (Newcastle), Lucas Digne (Paris St-Germain) Patrice Evra (Manchester United), Laurent Koscielny, Bacary Sagna (both Arsenal), Eliaquim Mangala (Porto), Mamadou Sakho (Liverpool), Raphael Varane (Real Madrid).

'Yan wasan tsakiya: Yohan Cabaye, Blaise Matuidi (both Paris St-Germain), Clement Grenier (Lyon), Rio Mavuba (Lille), Paul Pogba (Juventus), Moussa Sissoko (Newcastle), Mathieu Valbuena (Marseille).

'Yan wasan gaba: Karim Benzema (Real Madrid), Olivier Giroud (Arsenal), Antoine Griezmann (Real Sociedad), Loic Remy (Newastle, on loan from QPR), Franck Ribery (Bayern Munich).

Honduras:

Hakkin mallakar hoto AP

A karon farko a tarihinta, kasar Honduras ta tsallake zuwa gasar cin kofin duniya sau biyu a jere.

Kocin kasar Luis Fernando Suarez na saran samun nasara a wasa akalla daya saboda a tarihi kasar ba ta taba samun galaba a kan wata kasa ba a gasar cin kofin duniya.

Masu tsaron gida: Noel Valladares, Donis Escober (both Olimpia), Luis Lopez (Real Espana).

'Yan wasan baya: Brayan Beckeles (Olimpia), Emilio Izaguirre (Celtic), Juan Carlos Garcia (Wigan), Maynor Figueroa (Hull), Victor Bernardez (San Jose Earthquakes), Osman Chavez (Qingdao Janoon), Juan Pablo Montes (Motagua).

'Yan wasan tsakiya: Edder Delgado (Real Espana), Luis Garrido (Olimpia), Roger Espinoza (Wigan), Jorge Claros (Motagua), Wilson Palacios (Stoke), Oscar Garcia (Houston Dynamo), Andy Najar (Anderlecht), Mario Martinez (Real Espana), Marvin Chavez (Chivas USA).

'Yan wasan gaba: Jerry Bengtson (New England Revolution), Jerry Palacios (Alajuelense), Carlo Costly (Real Espana), Rony Martinez (Real Sociedad).