Ingila da Ecuador sun yi 2-2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sterling da Valencia na iya fuskantar hukuncin da zai shafi zuwansu gasar Kofin Duniya kan korarsu da aka yi

A wasannin sada zumunta na shirin gasar kofin duniya Ingila ta yi 2-2 da Ecuador, inda alkalin wasa ya kori Sterling da Valencia.

Valencia na Man United ne ya fara ci wa Ecuador minti takwas da fara wasa, kafin kuma Rooney ya rama bayan minti 21.

Sai kuma Lambert ya ci wa Ingila kwallo ta biyu a minti na 51, yayin da Arroyo ya farke cikin minti na 70.

Alkalin wasa ya kori Raheem Sterling na Liverpool dan Ingila saboda ketar da ya kai wa Valencia na Man United dan Ecuador,

wanda shi ma alkalin wasan ya sallama saboda hantarar Sterling din da ya yi.

Sauran wasannin da aka yi a daren na Laraba, Jamaica 2-2 Masar ; Netherlands 2-0 Wales

Algeria 2-1 Romania ; Hungary 1-0 Albania; Italy 1-1 Luxembourg.

Karin bayani