Fifa za ta binciki jami'an Qatar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rasha ce ta samu damar gasar 2018, Qatar kuma ta samu ta 2022 inda ta yi gakaba a kan Australia da Japan da Korea ta Kudu da kuma Amurka.

Mai bincike na Fifa, Micheal Garcia zai binciki jami'an kasar Qatar kan zargin da ake na ba da cin hanci don samun damar gudanar da gasar Kofin Duniya ta 2022 a kasar.

Jaridar Sunday Times ce ta yi zargin cewa Mohamed bin Hammam, tsohon mataimakin shugaban Fifa ya biya dala miliyan 5 ga jami'an Fifa domin zaben Qatar ta samu damar.

Amma tuni kwamitin nema wa Qatar damar ya musanta zargin inda ya kafe cewa Hammam bai yi abin da ake zargin ya yi ba da izinin kasar.

Garcia wanda lauya ne dan Amurka ya bayyana a farkon makon nan cewa zai kammala bincikensa kan zargin cin hanci wajen neman karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2018 da ta 2022 ranar tara ga watan Yuni.

Rasha ce ta samu damar gudanar da gasar 2018, Qatar kuma ta samu ta 2022 inda ta yi gakaba a kan Australia da Japan da Korea ta Kudu da kuma Amurka.