Rukunin G

Jamus:

Hakkin mallakar hoto Reuters

Tawagar 'German Machine' ta tsallake zuwa gasar bana ba tare da wata kungiya ta samu galaba a kanta ba a wasannin share fage inda ta zura kwallaye 36 cikin wasanni 10.

Jamus wacce ta lashe gasar hau sau uku sannan ta buga wasan karshe sau bakwai, na fatan cewar kocin 'yan wasan Joachim Low zai yi amfani da 'yan wasan Bayern Munich don tabbatar da nasarar kasar a wannan gasar a Brazil.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Manuel Neuer (Bayern Munich), Roman Weidenfeller (Borussia Dortmund), Ron-Robert Zieler (Hannover)

'Yan wasan baya: Jerome Boateng (Bayern Munich), Erik Durm (Borussia Dortmund), Kevin Grosskreutz (Borussia Dortmund), Benedikt Howedes (Schalke), Mats Hummels (Borussia Dortmund), Philipp Lahm (Bayern Munich), Per Mertesacker (Arsenal).

'Yan wasan tsakiya: Julian Draxler (Schalke), Matthias Ginter (Freiburg), Mario Gotze (Bayern Munich), Christoph Kramer (Borussia Monchengladbach), Sami Khedira (Real Madrid), Toni Kroos (Bayern Munich), Thomas Muller (Bayern Munich), Mesut Ozil (Arsenal), Marco Reus (Borussia Dortmund), Andre Schurrle (Chelsea), Bastian Schweinsteiger (Bayern Munich).

'Yan wasan gaba: Miroslav Klose (Lazio), Lukas Podolski (Arsenal).

Portugal:

Hakkin mallakar hoto Reuters

Wannan ne karo na shida da kasar Portugal za ta halarci gasar cin kofin duniya amma kuma ba ta taba kaiwa wasan karshe ba.

Gwarzon dan kwallon duniya Cristiano Ronaldo wanda ya taimaka mata ta tsallake zuwa gasar bana, na fama da rauni kuma idan har bai murmure ba, tabbas kasar za ta iya fuskantar matsala a gasar ta bana.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Beto (Sevilla), Eduardo (Braga), Rui Patricio (Sporting).

'Yan wasan baya: Andre Almeida (Benfica), Bruno Alves (Fenerbahce), Fabio Coentreo (Real Madrid), Joao Pereira (Valencia), Neto (Zenit), Pepe (Real Madrid), Ricardo Costa (Valencia).

'Yan wasan tsakiya: Joao Moutinho (Monaco), Miguel Veloso (Dinamo Kiev), Raul Meireles (Fenerbahce), Ruben Amorim (Benfica), William Carvalho (Sporting).

'Yan wasan gaba: Cristiano Ronaldo (Real Madrid), Eder (SC Braga), Helder Postiga (Lazio), Hugo Almeida (Besiktas), Nani (Manchester United), Rafa (Braga), Varela (FC Porto), Vieirinha (Wolfsburg).

Ghana:

Hakkin mallakar hoto Getty

Wannan ne karo na uku a jere da kasar Ghana za ta buga gasar cin kofin duniya, kuma tawagar ta Black Stars za ta nemi yin abinda ta yi a shekara ta 2010 inda ta kai matakin zagayen gabda na kusada karshe.

Kocin tawagar Kwesi Appiah zai kasance dan kasar Ghana na farko da zai ja ragamar zuwa gasar cin kofin duniya, kuma wasannin share fage kasar ta zura kwallaye 25.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Fatau Dauda (Orlando Pirates), Adam Kwarasey (Stromsgodset), Stephen Adams (Aduana Stars).

'Yan wasan baya: Samuel Inkoom (Platanias), Daniel Opare (Standard Liege), Harrison Afful (Esperance), John Boye (Rennes), Jonathan Mensah (Evian), Rashid Sumalia (Mamelodi Sundowns).

'Yan wasan tsakiya: Michael Essien (AC Milan), Sulley Muntari (AC Milan), Rabiu Mohammed (Kuban Krasnodar), Kwadwo Asamoah (Juventus), Emmanuel Agyemang-Badu (Udinese), Afriyie Acquah (Parma), Christian Atsu (Vitesse), Albert Adomah (Middlesbrough), Andre Ayew (Marseille), Mubarak Wakaso (Rubin Kazan).

'Yan wasan gaba: Asamoah Gyan (Al Ain), Kevin-Prince Boateng (Schalke 04), Abdul Majeed Waris (Valenciennes), Jordan Ayew (Sochaux).

Amurka:

Hakkin mallakar hoto Reuters

Kocin tawagar 'yan kwallon Amurka Jurgen Klinsmann ya ce burinsa shi ne ya kai kasar zuwa zagaye na biyu, kuma wannan ne karo na goma da kasar za ta buga gasar cin kofin duniya.

Duk da cewar bisa dukkan alamu Amurka na da rashin gogewa a 'yan wasanta na baya, amma dai za ta saran Clint Demsey ya haskaka don kasar ta taka rawar gani.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Brad Guzan (Aston Villa), Tim Howard (Everton), Nick Rimando (Real Salt Lake).

'Yan wasan baya: DaMarcus Beasley (Puebla), Matt Besler (Sporting Kansas City), John Brooks (Hertha Berlin), Geoff Cameron (Stoke City), Timmy Chandler (Nuremberg), Omar Gonzalez (LA Galaxy), Fabian Johnson (Hoffenheim), DeAndre Yedlin (Seattle Sounders).

'Yan wasan tsakiya: Kyle Beckerman (Real Salt Lake), Alejandro Bedoya (Nantes), Michael Bradley (Toronto FC), Brad Davis (Houston Dynamo), Mix Diskerud (Rosenborg), Julian Green (Bayern Munich), Jermaine Jones (Besiktas), Graham Zusi (Sporting Kansas City).

'Yan wasan gaba: Jozy Altidore (Sunderland), Clint Dempsey (Seattle Sounders), Aron Johannsson (AZ Alkmaar), Chris Wondolowski (San Jose Earthquakes).