Rukunin H

Belgium:

Hakkin mallakar hoto AP

Kasar Belgium ta yi matukar haskakawa a wasannin share fage na neman cancantar buga gasar ta bana saboda babu kasar da ta doke ta, kuma wannan ne karo na shida da za ta halarci gasar kofin duniya.

Kocin tawagar 'yan kwallonta, Marc Wilmots wanda ya shafe shekaru biyu tare da tawagar na saran irinsu Eden Hazard da Vincent Kompany su taka rawar gani don kasar ta bada mamaki a wannan gasar.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Thibaut Courtois (Atletico Madrid, on loan from Chelsea), Simon Mignolet (Liverpool), Koen Casteels (Hoffenheim), Silvio Proto (Anderlecht).

'Yan wasan baya: Toby Alderweireld (Atletico Madrid), Laurent Ciman (Standard Liege), Nicolas Lombaerts (Zenit St Petersburg), Vincent Kompany (Manchester City), Daniel Van Buyten (Bayern Munich), Anthony Vanden Borre (Anderlecht), Thomas Vermaelen (Arsenal), Jan Vertonghen (Tottenham).

'Yan wasan tsakiya: Nacer Chadli, Mousa Dembele (both Tottenham), Steven Defour (Porto), Kevin De Bruyne (Wolfsburg), Marouane Fellaini, Adnan Januzaj (both Manchester United), Eden Hazard (Chelsea), Kevin Mirallas (Everton), Divock Origi (Lille), Axel Witsel (Zenit St Petersburg).

'Yan wasan gaba: Romelu Lukaku (Everton, on loan from Chelsea), Dries Mertens (Napoli).

Algeria:

Hakkin mallakar hoto AP

Kasar Algeria ce kadai kasar Larabawa a nahiyar Afrika da za ta halarci gasar cin kofin kwallon Afrika a bana.

Zinedine Zidane, Karim Benzema da Samir Nasri duk 'yan asalin Algeria ne amma kuma basu taba buga mata kwallo ba, sai dai a gasar bana za ta sa'ido a kan Sofiane Feghouli domin kaiwa ga nasara.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Rais Mbolhi (CSKA Sofia), Cedric Si Mohamed (CS Constantine), Mohamed Lamine Zemmamouche (USM Alger).

'Yan wasan baya: Essaid Belkalem (Watford, on loan from Granada), Madjid Bougherra (Lekhwya Club), Liassine Cadamuro (Mallorca), Faouzi Ghoualm (Napoli), Rafik Halliche (Academica Coimbra), Aissa Mandi (Stade Reims), Carl Medjani (Valenciennes), Djamel Mesbah (Livorno), Mehdi Mostefa (AC Ajaccio).

'Yan wasan tsakiya: Nabil Bentaleb (Tottenham), Yasine Brahimi (Granada), Medhi Lacen (Getafe), Saphir Taider (Inter Milan), Hassan Yebda (Udinese).

'Yan wasan gaba: Abdelmoumene Djabou (Club Africain), Sofiane Feghouli (Valencia), Nabil Ghilas (Porto), Riyad Mahrez (Leicester City), Islam Slimani (Sporting Lisbon, Portugal), Hilal Soudani (Dinamo Zagreb).

Rasha:

Rasha wacce za ta dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 na saran soma nuna wa duniya cewar ita ba kanwan lasa bace.

Tawagar 'yan kwallon kasar karkashin jagorancin Fabio Capello tana saran kaiwa akalla matakin zagaye na biyu domin share fagen gasar da ke tafe shekaru hudu masu zuwa.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Igor Akinfeev (CSKA Moscow), Yury Lodygin (Zenit St Petersburg), Sergey Ryzhikov (Rubin Kazan).

'Yan wasan baya: Vasili Berezutskiy (CSKA Moscow), Vladimir Granat (Dynamo Moscow), Andrey Eshchenko (Anzhi Makhachkala), Sergey Ignashevich (CSKA Moscow), Alexey Kozlov (Dynamo Moscow), Dmitry Kombarov (Spartak Moscow), Andrey Semenov (Terek Grozny), Georgi Schennikov (CSKA Moscow).

'Yan wasan tsakiya: Denis Glushakov (Spartak Moscow), Igor Denisov (Dynamo Moscow), Alan Dzagoev (CSKA Moscow), Yury Zhirkov (Dynamo Moscow), Alexey Ionov (Dynamo Moscow), Alexander Samedov (Lokomotiv Moscow), Victor Faizulin (Zenit St Petersburg), Oleg Shatov (Zenit St Petersburg), Roman Shirokov (Krasnodar).

'Yan wasan gaba: Maxim Kanunnikov (Amkar Perm), Alexander Kerzhakov (Zenit St Petersburg), Alexander Kokorin (Dynamo Moscow).

Koriya ta Kudu:

Tun daga shekara ta 2002 lokacin da Koriya ta Kudu ta dauki bakuncin gasar kofin duniya tare da Japan, kasar ta soma haskakawa fagen tamaular duniya.

Wannan ne karo na takwas da kasar za ta buga gasar cin kofin duniya kuma babban dan wasanta Son Heung-min wanda ke taka leda a Bayer Leverkusen shi ne za a sawa ido domin kaiwa ga nasara.

Tawaga:

Masu tsaron gida: Jung Sung-ryeong (Suwon Bluewings), Kim Seung-gyu (Ulsan Horang-i), Lee Bum-young (Busan I'Park)

'Yan wasan baya: Yun Suk-young (QPR), Kim Young-kwon (Guangzhou Evergrande), Hwang Seok-ho (Sanfrecce Hiroshima), Hong Jeong-ho (Augsburg), Kwak Tae-hwi (Al Hilal), Lee Yong (Ulsan Horang-i), Kim Chang-soo (Kashiwa Reysol), Park Joo-ho (Mainz)

'Yan wasan tsakiya: Ki Seung-yueng (Sunderland, on loan from Swansea), Ha Dae-sung (Beijing Guoan), Han Kook-young (Kashiwa Reysol), Park Jung-woo (Guangzhou R&F), Son Heung-min (Bayer Leverkusen), Kim Bo-kyung (Cardiff City), Lee Chung-yong (Bolton Wanderers), Ji Dong-won (Augsburg).

'Yan wasan gaba: Koo Ja-cheol (Mainz), Lee Keun-ho (Sangju Sangmu), Park Chu-young (Arsenal), Kim Shin-wook (Ulsan Horang-i).