Tennis:Sharapova da Halep a wasan karshe

Image caption A ranar Asabar za su fafata wasan karshen,

Maria Sharapova ta kai wasan karshe na gasar tennis ta Faransa karo na uku a jere, inda za ta fafata da Simona Halep ta Romania.

Wannan shi ne karon farko da Simona Halep mai shekara 22, kuma ta 57 a duniya amma ta hudu a kasarta ta kai wasan karshe na babbar gasa.

Sharapova, 'yar Rasha, ta biyu a duniya ta doke Eugenie Bouchard da ci 4-6, 7-5 da 6-2, yayin da Halep ta doke Andrea Petkovic ta Jamus da ci 6-2, 7-6 (7- 4).

Sharapova wadda ta dauki kofin gasar a 2012 ta yi galaba a kan Bouchard ta bakwai a duniya mai shekaru 20 'yar kasar Canada cikin sa'o'i biyu da minti 27.