Kofin Duniya:Ingila na rukuni mafi karfi

Image caption Ingila za ta fara wasanta ranar 14 ga watan Yuni da Italiya a Manaus

Ingila na cikin rukuni mafi wahala a gasar cin kofin duniya, yayin da Najeriya ke rukuni mafi rauni kamar yadda jadawalin karfin kasashe na Fifa na watan Yuni ya nuna.

Ingilan wadda ta matsa daga ta tara a duniya zuwa ta goma a watan nan tana rukuni na hudu (Group D) da Uruguay ta bakwai da Italiya ta tara sai kuma Costa Rica ta 28 a duniya.

Rukunin na Ingila shi kadai ne ya kunshi kasashen da suke cikin jerin goma na farko a duniya na jadawalin na Fifa.

Argentina wadda take ta biyar a duniya na cikin rukunin da yake mafi rauni a gasar ta duniya, wanda ya kunshi Bosnia-Herzegovina ta 21 da Iran ta 43 da kuma Najeriya ta 44, yayin da Australia ta 62 ta kasance kasa mafi rauni a gasar gaba daya.