Liverpool ta amince ta sayi Can

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya dauki hankalin kocin Liverpool Brendan Rodgers ta hanyar burge shi da salon wasansa.

Kungiyar Liverpool ta amince da cinikin dan wasan Jamus na tawagar 'yan kasa da shekara 21 kuma na kungiyar Bayern Leverkusen Emre Can.

Can mai shekaru 20, wanda ya fi son buga wasan tsakiya, zai koma Liverpool kan kudi fam miliyan 10.

Za a kammala cinikin dan wasan da zarar an rattaba hannu kan takardun kwantiragin.

Can wanda dan asalin kasar Turkiya ne, ya koma Leverkusen ne daga Bayern Munich a bara kan kudi fam miliyan hudu.