Qatar 2022 Platini ya ce a iya sake zabe

Hakkin mallakar hoto u
Image caption Platini ya ce idan aka tabbatar da zargin za a sake zaben tare da saka takunkumi.

Shugaban hukumar Uefa Michel Platini ya yi kira da a sake gudanar da zabe kan kasar da za ta karbi bakuncin gasar cin kofin duniya a 2022 matukar zargin da ake wa Qatar na ba da cin hanci ya tabbata.

Bukatar gudanar da binciken ta biyo bayan wani rahoto da jaridar Sunday Times ta fitar na zargin da ake wa jami'an hukumar Fifa kan batun karbar na goro domin amince wa Qatar ta karbi bakuncin gasar.

Shi ma shugaban Hukumar kwallon kafa ta Turai Platini Qatar ya zaba, kuma ya ce bai yi nadamar hakan ba tun da Qatar ita ce zabin Fifa.

Sai dai kwamatin neman karbar bakuncin gasar na kasar ta Qatar ya musanta zargin.