Qatar 2022: Fifa za ta yanke hukunci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Blatter ya ce lauyan zai gabatar da jawabi a babban taron Fifa da za a fara ranar Talata kan abin da ya gano kawo yanzu.

Shugaban Fifa Sepp Blatter ya ce hukumar za ta zartar da hukunci kan yadda aka gudanar da zaben kasashen da za su karbi bakuncin gasar kofin duniya ta 2018 da ta 2022 a watan Satumba ko Oktoba.

Shugaban hukumar kawllon kafar ta duniya ya ce a wannan lokacin ne za a kawo karshen maganar zargin da ake cewa Qatar ta bayar da cin hanci domin ba ta gasar 2022.

A watan Disamba na 2010 ne aka zabi kasar ta Qatar inda ta yi galaba a kan Australia da Japan da Korea ta Kudu da kuma Amurka.

A halin da ake ciki wani lauyan Amurka Micheal Garcia yana gudanar da bincike mai zaman kansa kan yadda aka gudanar da ba da gasar kuma zai gabatar da rahotonsa a tsakiyar watan Yuli.

Sepp Blatter ya ce lauyan zai gabatar da jawabi a babban taron Fifa da za a fara ranar Talata inda zai yi wa mahalatta taron bayani kan abubuwan da ya gano kawo yanzu.