AC Milan: Inzaghi ya canji Seedorf

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Seedorf mai shekara 38 ya maye gurbin Massimiliano Allegri a watan Janairu yayin da kungiyar take ta 11 a gasar Serie A.

AC Milan ta kori kociyanta Clarence Seedorf kasa da watanni biyar da nada shi ta kuma bayyana Filippo Inzhagi ya maye gurbinsa.

Inzaghi mai shekaru 40, tsohon dan wasan gaba na Italiya ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da ya bar matsayinsa na kocin matasan kungiyar ya koma na manya.

Seedorf mai shekara 38 ya maye gurbin Massimiliano Allegri a watan Janairu yayin da kungiyar take ta 11 a gasar Serie A.

Seedorf, tsohon dan wasan Holland ya yi nasarar cin 11 daga cikin wasanni 19 da ya jagoranci kungiyar da ya shiga a matsayin dan wasa a 2002, shekara daya bayan Inzaghi.

AC Milan ta dauki kofunan Serie A biyu da na Zakarun Turai biyu lokacin Inzaghi da Seedorf suna 'yan wasa.