Zanga-zanga a Sao Paulo na Brazil

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Brazil na fuskantar barazana daga masu zanga-zanga a daidai lokacin da a ke kokarin fara gasar cin kofin duniya.

'Yan Sandan kwantar da tarzoma a Birnin Sao Paulo na Brazil, sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa ma su zanga-zanga kwanaki uku suka rage a bode gasar cin kofin duniya a Babban filin kwallo dake birnin.

Wakilin BBC Katy Watson wanda ya gane ma idanunsa, ya bayyana cewa a kalla ma su zanga- zangar kimanin 300 ne suka fito, haka kuma jirage ma su sukar ungulu na shawagi a sararin samaniya.

Kungiyar ma'aikatan karafa ta Sao Paulo da ma'aikatan ta ke yajin aiki kan karin kashi 12.2 cikin dari na albashinsu ce ta kira zanga-zangar.

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta ce, ba za ta kyale ma su zanga-zangar ba su kawo cikas a gasar cin kofin duniya da za a fara nan da kwanaki 3.