'Yan wasan Kamaru sun isa Brazil

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kamaru na rukuni farko watau (Group A) inda za ta fafata da Brazil da Croatia da kuma Mexico.

Yanzu haka 'yan wasan kasar Kamaru sun sauka a Brazil don fara gasar cin kofin duniya bayan turjiyar da suka yi tun da farko sakamakon rashin biyansu kudaden alawus-alawus.

Tawagar da ta hada da dan wasan gaban Chelsea Samuel Eto'o, tun da farko shi ma ya ki tashi zuwa kasar Amurka ta kudu,amma daga bisani an samu daidaito tsakanin 'yan wasan da hukumar kwallon kafa ta kasar bayan wata ganawar gaggawa.

Tawagar 'yan wasan Kamarun sun isa Brazil ranar Lahadi da misalin karfe 9:30 na dare.

Kocin Kamaru Volker Finke ya bayyana cewa 'yan wasan na kokawa ne kan karancin kudin alawus na fam dubu 61 domin shiga wasan.