Faransa ta ci Jamaica 8-0

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kasar Faransa za ta hadu da Honduras da Switzerland da Ecuador a rukuni na biyar watau (Group E).

Kungiyar kwallon kasar Faransa ta zura kwallaye 3 kafin hutun rabin lokaci, a wasan karshe na sharar fagen gasar cin kofin duniya da ta yi da Jamaica ranar Lahadi, ta hannun tsohon dan wasan tsakiyar Newcastle Yohan Cabaye da Blaise Matuidi da kuma Karim Benzema.

Haka nan 'yan wasa irinsu Matuidi and Benzema sun ci kwallaye bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, inda Giroud da Antoine Griezmann suka karasa cin ragowar kwallayen.

Dan wasan tsakiyar Real Madrid Benzama ya nuna farin cikinsa ganin yadda faransa ta nuna za ta iya tabuka abin kirki duk da rashin Frank Ribery wanda ba zai buga gasar ba saboda ciwon baya da yake fama da shi..

Sauran 'yan wasan da za su wakilci Faransar sun hada da dan wasan Tottenham Hotspur's Hugo Lloris da na Manchester United Patrice Evrasai da na Liverpool Mamadou Sakho da kuma na Newcastle Moussa Sissoko wadanda ke kan gaba a jerin 'yan wasan.