'Ingila da Brazil su na da dama iri daya'

Hakkin mallakar hoto d
Image caption Pele na son ganin an yi wasan karshe tsakanin Brazil da Uruguay a gasar cin kofin duniya ta 2014.

Shahararren dan kwallon Brazil watau Pele, ya ce Ingila na da dama irin wacce Brazil ke da ita a gasar cin kofin duniya ta 2014

Pele mai shekaru 73, ya yi fatan kasarsa ta hadu da Uruguay a wasan karshe don daukar fansar abin da ya faru a gasar 1950.

Da aka tambaye shi dangane da damar da Ingila ke da ita, Pele ya bayyana cewa, "Ingila kamar Brazil ce da Italiya da Faransa wadanda dukkanin su shahararru ne saboda haka dole ne mu shirya."

Pele wanda ya dauki kofin duniya sau uku tare da Brazil, ana kuma daukar sa a matsayin dan kwallon da ya fi shahara a duniya, ya kara da cewa,"dole mu girmama Ingila wacce ke da irin damar da muke da ita.