Wilshere: Mun shirya wa Pirlo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Italiya ta fitar da Ingila a gasar kofin Turai ta 2012

Jack Wilshere ya ce hana Andrea Pirlo sakat shi ne babban abin da Ingila za ta mayar da hankali a kai a wasansu na farko na cin kofin duniya da Italiya ranar Asabar a Manaus.

Dan wasan tsakiyar na Italiya mai shekaru 35 ya wahalar da Ingila inda Italiyan ta yi galaba a kansu a bugun fanareti na wasan dab da na kusa da karshe na kofin Turai na 2012.

Wilshere ya ce Ingila ta yi duk shirin da ya kamata a wasanninta na sada zumunta.

Dan wasan na Arsenal ya kara da cewa, '' mun san Pirlo gwani ne wanda ke tafiyar da wasa amma ba za mu sake da shi ba.''