Uefa ta bukaci Blatter ya sauka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Blatter ya gana da jami'an Uefa ne bayan da sauran hukumomi biyar na Fifa su ka goyi bayansa ya sake takara.

Shugabannin hukumar kwallon kafa ta Turai sun bukaci shugaban Fifa Sepp Blatter ya sauka daga mukaminsa a shekara mai zuwa saboda bata sunan Fifa da cin hanci.

Ana dai zargin cewa kasar Qatar ta bayar da cin hanci domin samun damar karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2022.

Micheal Van Praag, shugaban hukumar kwallon Holland, ya ce, Fifa ta dulmiya cikin rashawa karkashin Sepp Blatter, wanda ya ce ka da ya tsaya zabe a 2015.

Ya kara da cewa, Fifa ba za ta iya farfado da martabarta ba har sai Blatter ya sauka daga mukaminsa.

Shi kuwa shugaban hukumar kwallon Ingila, Greg Dyke suka yayi ga zargin da Blatter ya yi cewa, akwai wariya cikin zargin cewa Qatar ta ba da cin hanci kafin ta samu damar karbar bakuncin gasar kofin duniya ta 2022.

Blatter ya gana da jami'an Uefa ne a wurin babban taron Fifa a Sao Paulo bayan da sauran hukumomin kwallon kafa biyar na Fifa su ka goyi bayansa ya sake takara.

Karin bayani