Pacquiao: Ya zama kocin kwallon kwando

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu na korafi kan nadin da aka yi wa Manny Pacquiao din

An nada Manny Pacquiao zakaran damben boksin na duniya na ajin matsakaita nauyi (welterweight) a matsayin sabon kocin kwallon kwando na kasar Philippines.

Bayan nadin nasa Pacquiao, ya ce yana son nuna wa duniya cewa hazakarsa ba ta tsaya kan damben boksin ba kadai har ma da kwallon kwando.

Zakaran damben na duniya ya kuma ce wasan dambe da kuma na kwallon kwando abubuwa ne da ke a ransa.

A watan Oktoba ne za a fara kakar wasannin kwallon kwando ta 2014-15 ta Philippines din kuma a watan Nuwamba ne sabon kocin zai yi dambe.