Cristiano Ronaldo ya dawo wasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cristiano Ronaldo

Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo, ya dawo wasa da kafar dama bayan ya warke daga raunin da ya ji inda ya taimaka wa Portugal ta doke Jamhuriyar Ireland a wasan sada zumunci.

Ronaldo mai shekaru 29, bai buga wasannin sada zumunta biyu da Portugal din ta yi sakamakon ciwon gwiwa da kuma cinya, amma duk da haka ya yi wasan minti 66.

Kocin Portugal Paulo Bento ya fadi cewa, "buga wasan da ya yi na da muhimmanci don ba za mu boye ba. Mun ji dadin dawowarsa."

Portugal za ta fara wasanta a rukunin na bakwai wato Group G inda za ta fafata da kasar Jamus ranar Litinin.

Ronaldo bai ci wa portugal kwallo ba amma ya buda wa dan wasan gaba Hugo Almeida wanda ya ci kwallaye biyu inda ya fara daga raga da bugun tazara kafin tafiya hutun rabin lokaci.

Karin bayani