Rooney: Welbeck zai yi wasan Italiya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rooney ya ce ,''zai murmure sosai ''

Wayne Rooney ya ce Danny Welbeck zai samu sauki har ya yi wasan Ingila na farko a gasar kofin duniya da Italiya ranar Asabar.

Welbeck mai shekaru 23 ya ji rauni a cinyarsa lokacin atisaye ranar Talata abin da ya sa bai yi atisayen ba ranar Laraba a Rio.

Rooney na magana ne domin kawar da fargaba kan dan wasan na Man United wanda ya ci wa Ingila kwallo takwas a wasanni 20 karkashin Roy Hodgson.

Rashin Welbeck zai kara damar Raheem Sterling na Liverpool ta buga wasan da Italiya.