Ingila na nazarin raunin Welbeck

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Danny Welbeck

Ingila za ta ba da bayani dangane da dan wasan ta Danny Welbeck wanda ya ji raunin da ya damu kasar, ganin yadda za ta fara wasanta na farko a gasar kofin duniya da kasar Italiya a ranar Asabar.

Welbeck, dan wasan gaban Man United, mai shekaru 23, an bayyana cewa ya ji rauni a kafa yayin da suke horo a sansaninsu da ke Urca ranar Talata.

Idan aka cire Welbeck daga tawagar ta Ingila hakan zai kara wa dan wasan gefe na Liverpool Raheem Sterling damar fuskantar Italiya a Manaus.

Welbeck ya ci kwallaye 8 a wasanni 20 da ya buga karkashin kocin Ingila Roy Hodgson.

Saboda haka rashin Welbeck cikin tawagar Ingilar cikas ne ga kocin tawagar Roy Hodgson a kokarin Ingila na taka rawar gani a gasar.

Karin bayani