Ingila na dari-dari da Balotelli

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rashin tabbas a kan Balotelli na daga dalilan da za su sa Ingila sanya ido a kansa.

Joe Hart da Gary Cahill sun ba wa tawagarsu ta gasar kofin duniya shawarar sanya ido sosai a kan Mario Balotelli a wasan Ingila da Italiya ranar Asabar.

Tsohon abokin wasan Hart a Manchester United, Balotelli na daya daga cikin 'yan wasan da suka taimaka wa Italiya zuwa wasan karshe na gasar kofin Turai ta 2012.

Hart ya ce, ''dan wasa ne da yake kamar mazari wanda ba a san gabansa ba.''

Shi ma Cahill ya kara da cewa, ''Mario dan wasa ne da ba za ka iya hasashe a kansa ba.

Na kara da shi a wasa a lokacin da ya yi kokari, na kuma kara da shi a lokacin da ka fitar da shi bayan minti 60. Abu ne me wuya ka ce ga yanayinsa.''