Sepp Blatter ya kalubalanci Uefa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Blatter dai na kara fuskantar matsin lamba kan batun zargin cin hanci a baiwa Qatar damar karbar bakuncin gasar 2022

Shugaban Fifa Sepp Blatter, ya nuna bukatarsa ta neman kujerar shugabancin Fifa karo na biyar ya kuma bayyana matakin da Uefa ta yi na ya sauka da zarar ya kammala wa'adinsa a matsayin halin rashin da'a.

A na dai kalubalantar sa ne kan matsalar rashawa da cin hanci da ta damu hukumar ta kwallon kafa.

Sai dai Blatter, dan kasar Swiss, mai shekaru 78 ya ce, ya yi bakin ciki musamman yadda wasu daga cikin shugabannin kwallon Turai da suka yi kira ya sauka daga mukamin na sa.

Blatter ya kuma fadawa mahalarta Babban taron da Fifa ta yi cewa "wannan shine wani abu na rashin da'a da ya taba gani a rayuwarsa."

Wannan mataki da ya ke kokarin dauka, na da alaqa da hukuncin da Fifa ta yanke wanda ke nuni da cewa, ba bu adadin shekaru ko lokaci a ka shugabin cin Fifa da za su hana mutum tsayawa takara mattukar yana da sha'awa.