Brazil ta doke Croatia da 3 da 1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Brazil na murnar nasara a kan Croatia

Neymar ya haskaka a wasan da Brazil ta doke Croatia da ci uku da daya a wasan farko na bude gasar cin kofin duniya da aka buga a birnin Sao Paulo.

Duk da cewar Croatia ce ta soma shiga gaba a wasan inda Mercelo ya ci kansu amma daga bisani Neymar ya farkewa Brazil sannan kuma ya ci wa kasar kwallo ta biyu a bugun fenariti bayan an dawo hutun rabin lokaci.

Oscar wanda ke taka leda a Chelsea shi ne ya ci wa Brazil kwallo ta uku a minti na 90.

A ranar Juma'a za a buga wasanni uku a gasar inda Kamaru za ta fafata da Mexico, sai wasa tsakanin Spain da Netherlands a yayinda ita kuma Chile za ta kece raini da Australia.

Karin bayani