Kamaru za ta kece raini da Mexico

'Yan wasan kasar Kamaru Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kamaru ce kasa ta farko a Afirka da za ta fara wasa a gasar

Kasar Kamaru za ta fafata da Mexico a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a ranar Juma'a.

Sai dai akwai yiwuwar Kamaru wadda ita ce kasar Afurka ta farko da za ta fara karawa a gasar, za ta yi karawar ba tare da wasu zaratan 'yan wasanta ba.

Babu tabbas, ko kyaftin din kungiyar Samuel Eto'o zai taka leda a wasan na ranar Juma'a, saboda rashin halartar cikakken atisaye a makonnin da suka gabata.

A lokaci guda kuma, dan wasan tsakiya Jean Makoun bai dade da komawa kungiyar ba, sakamakon raunin da ya yi fama da shi a gwiwa, don haka da wuya ya buga wasan da Mexico.

Ayarin 'yan wasan Kamaru sun isa Brazil a makare, kwanaki hudu kacal kafin wasansu, bayan sun ki hawa jirgin da zai kai su har da aka sasanta rikici kan kudadensu na alawus.

Sai dai kocin Mexico, Miguel Herrera ya tabbatar da cewa shi ma dan wasan gaban kungiyarsa, Javier Hernandez ba zai buga wasa da Kamaru ba, saboda rashin jefa ko da kwallo daya a wasanni tara da ya buga.