Birtaniya za ta kara tallafin yakar Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar ta kaddamar da karin hare-hare tun 2009 a yunkurinta na kafa kasar musulunci a Najeriya.

Sakataren wajen Birtaniya, William Hague ya ce kasar za ta kara tallafin aikin soja da harkar ilmi ga Najeriya don tunkarar Boko Haram.

Ya ce dakarun sojan Najeriya za su samu karin horo musammam kan sha'anin yaki da ta'addanci, kuma karin yara miliyan daya za su samu tallafin karatu.

Wannan shi ne alkawari na baya-bayan nan daga taimakon kasashen yamma, tun bayan sace 'yan matan Chibok sama da 200 da 'yan Boko Haram suka yi a watan Afrilu.

Tun daga nan, kungiyar ta kara yawan hare-haren da take kai wa a kasar.

William Hague ya yi wannan jawabi ne a wani taron koli da ke gudana a London kan batun kungiyar Boko Haram.

Taron ya biyo bayan wanda ya gabata ne cikin watan jiya a Paris, inda kasashe makwabtan Najeriya suka yi alkawarin aiki tare don kawar da Boko Haram.

Kungiyar ta kaddamar da karin munanan hare-hare tun shekara ta 2009 a yunkurinta na kafa kasar musulunci a Najeriya.

Dubban mutane ne suka halaka a hare-harenta da kuma yunkurin jami'an tsaro da ya biyo baya na murkushe ta.

Karin bayani