Mexico ta doke Kamaru da ci 1 da 0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Oribe Peralta na murnar zura kwallo

Mexico ta samu galaba a kan Kamaru da ci daya mai ban haushi, a wasan da suka buga na gasar cin kofin duniya.

Oribe Peralta wanda ke bugawa kungiyar Santos Laguna ne ya ci kwallon a minti na 74.

A lokacin wasan Mexico ta zura kwallaye biyu a yayinda Kamaru ta zura daya amma kuma alkalin wasa ya ce dukansu sun yi satar gida.

'Yan wasan Kamaru, Samuel Eto'o da kuma Benoit Assou-Ekotto duk sun kai harin cin kwallo amma kuma babu sa'a.

Wannan sakamakon ya nuna cewar Mexico na da maki uku inda ta ke matakin na biyu a rukunin A, saboda Brazil ta fita yawan kwallaye.

Karin bayani