Sagna zai koma Manchester City

Bacary Sagna Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwantiragin dan Faransan ya kare a karshen kakar wasanni

Manchester City ta cimma yarjejeniyar sayen dan wasan baya na Arsenal, Bacary Sagna.

Dan wasan wanda zai koma Man city, bayan kammala gasar cin kofin duniya a Brazil, ya buga sakon ban kwana ga Arsenal a shafinsa na zumunta.

Tuni dai, aka ba shi riga mai lamba uku da yake sanyawa a tsohuwar kungiyarsa, wadda tsohon dan wasan bayan Brazil, Maicon ya sa a Man City.

A watan yulin shekara ta 2007 ne, Arsenal ta biya Auxerre fam miliyan bakwai a kan Sagna.

Ya buga wasanni 284 a shekaru bakwai da ya yi a Arsenal, kuma sau biyu ana zabarsa cikin ayarin kungiyar gasar Firimiya ta shekara.