Argentina ta kusa gane kurenta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wankin hula ya kusa kai Argentina dare a wasan da suka yi da kasar Bosnia.

A ci gaba da gasar cin kofin duniya da ake a Brazil, kasar Argentina ta kwaci kanta da kyar a hannun Bosnia a fafatawar da suka yi aka tashi wasan ci 2-1.

Argentiana ta samu nasarar kwallo ta farko bayan da dan wasan baya na kasar Bosnia Sead Kolasinac mai lamba biyar ya ci kan su bisa kuskure.

Lionel Messi ya ci kwallo ta biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci wacce ta kara wa 'yan wasan karsashi.

Duk da haka 'yan wasan Bosnia ba su gajiya ba inda ana dab da tashi daga wasan, Vedad Higuain ya jefa kwallo a ragar Argentina.