Belgium ta doke Algeria 2-1

Belgium ta doke Algeria 2-1 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Algeria ce ta fara zira kwallon ta bugun fanareti

Kwallaye biyun da Marouane Fellaini da Dries Mertens suka zira sun baiwa Belgium nasara a kan Algeria a rukunin H na gasar cin kofin duniya.

Algeria ce ta fara zira kwallo ta hannun Sofiane Feghouli daga bugun fanareti bayan da dan wasan Tottenham Jan Vertonghen ya tade shi.

Dan wasan Manchester United Fellaini ya farke da ka, jim kadan bayan da aka sako shi bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Sai kuma Mertens ya zira ta biyu bayan wata zari-zuga da suka yi.

Rukunin na H ya kunshi Belgium da Algeria da Rasha da kuma Koriya ta Kudu.

Karin bayani