Brazil ta tashi canjaras da Mexico

Hakkin mallakar hoto Getty

Mai masaukin baki Brazil ta tashi canjaras a wasanta na biyu da Mexico a rukunin A, a ci gaba da gasar cin kofin duniya.

Duka bangarorin biyu sun kai hare-hare amma babu wanda ya samu damar zura kwallo.

Sau biyu Neymar yana kai farmaki mai karfi yayin da Raul Jimenez na Mexico ya kusa zira kwallo a ragar Brazil ana dab da tashi.

A yanzu Brazil ce kan gaban Mexico a rukunin da tazarar kwallaye bayan da dukkansu ke da maki hudu-hudu.

A ranar Laraba ne Kamaru za ta kara da Croatia - duka kasashen biyu sun sha kayi a wasansu na farko.

Karin bayani