Draxler ya yi watsi da tayin zuwa Arsenal

Julian Draxler Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Draxler na cikin tawagar Jamus ta gasar cin kofin duniya

Dan wasan Schalke Julian Draxler ya ce ya yi watsi da tayin zuwa Arsenal a watan Janairu kuma zai ci gaba da kasance wa a Jamus.

Draxler, dan wasan na Jamus mai shekaru 20, an yi hasashen zai koma Arsenal a kakar musayar wasanni.

Bayan da ya sanya hannu a kwantiragin shekaru biyar a Schalke a watan Mayu, ya ce "An yi min tayin komawa Arsenal amma na yi watsi da ita.

"Zan sake yin hakan a bana. Ina so na sake taka leda ta shekara daya a Schalke."

Karin bayani