Rouhani ya jinjina wa 'yan wasan Iran

Gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a Brazil Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan wasan Super Eagles na Nigeria sun fi rike kwallo a wasan su da Iran

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya jinjinawa 'yan wasan kasarsa game da canjaras ba ci da suka yi da Nigeria a gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da aka buga ranar Litinin a Brazil.

A tsokacin da ya rubuta a shafinsa na Twitter a ranar Talata, shugaba Rouhani ya ce yana alfahari da maki gudan da 'yan wasan suka samu, inda ya ce yana fatan za su yi galaba a wasan da za su buga a nan gaba.

Wasu masana harkar wasanni sun ce a wasan da aka buga a birnin Curitiba na Brazil 'yan wasan Super Eagles sun fi rike kwallo amma kuma suka kasa zura kwallo a wasan.

'Yan wasan Najeriyar kamar su Ogenyi Onazi da Ahmed Musa da kuma Shola Ameobi duk sun kusa zura kwallaye a wasan.

A bangaren Iran kuwa, dan wasan kasar Reza Ghoochannejad shi ne ya kai hari mafi hadari, amma kuma mai tsaron gida na Super Eagles Vincent Enyeama ya kabe ta.

A yanzu Argentina ce ke kan gaba a rukunin, sai Nigeria da Iran a matsayi na biyu, yayin da Bosnia ke matakin karshe.