Okocha ya caccaki Keshi

Mai horas da 'yan wasan Nigeria Stephen Keshi
Image caption Wasu masana sun ce Keshi ya yi kuskure a wasansu da Iran.

Tsohon dan wasan Nigeria Austin Jay-Jay Okocha ya dora alhakin rashin cin kwallon da 'yan Nigeria suka yi a wasansu da Iran a kan mai horas da 'yan wasan na Super Eagles Stephen Keshi.

Jay-Jay Okocha ya ce kamata ya yi Nigeria ta lashe wasanta da Iran amma kasar ta gaza yin hakan.

A cewar Okocha, Keshi bai yi aiki sosai ba akan 'yan wasan, kuma ya yi kuskure da ya sauya Victor Moses da Shola Ameobi bayan hutun rabin lokaci.

A ranar asabar ne Nigeria za ta buga wasanta na biyu da kasar Bosnia-Hercegovina, wacce ta sha kashi a hannun Argentina da ci 2-1.