Gasar cin kofin duniya: Rana ta shida

Gasar cin kofin duniya: Rana ta shida Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kawo yanzu dai komai na tafiya yadda ya kamata a Brazil

A rana ta shida ta gasar cin kofin duniya, masu masaukin baki Brazil za su sake shiga fagen daga inda za su fafata da Mexico.

Sai dai kafin sannan Belgium za ta kara da Algeria sannan Rasha za ta kece raini da Koriya ta Kudu a rukunin H.

Daga yau za a iya fahimtar inda al'amura suka dosa inda za a iya ganin kamun ludayin kowacce kasa daga cikin kasashe 32 da ke halartar gasar.

Su waye za su fafata kuma waye zai yi nasara?

Belgium da Algeria (17 June, 17:00 BST)

Hasashen mai yiwa BBC sharhi kan al'amuran wasanni Mark Lawrenson: Belgium 2-0 Algeria

Brazil da Mexico (17 June, 20:00 BST)

Hasashen Mark Lawrenson: Brazil 2-0 Mexico

Rasha da Koriya ta Kudu (17 June, 23:00 BST)

Hasashen Mark Lawrenson: Rasha 2-0 Koriya ta Kudu

Sai ku kasance da shafin bbchausa.com domin samun sharhi da rahotanni kai tsaye game da wasan da za a kara tsakanin Brazil da Mexico da ma sauran labaran da suka shafi gasar.

Karin bayani