Kofin Duniya: Kamaru ta yi waje

Hakkin mallakar hoto Getty

Croatia ta fitar da Kamaru daga gasar cin kofin duniya bayan ta cinye ta 4 da nema a wasa na biyu na rukunin A.

Tun a minti na 11 ne dan wasan Croatia Ivica Olic ya fara jefa kwallo a ragar Kamaru, sai dai lamarin ya kara kazance mata lokacin da alkalin wasa ya kori Alex Song a minti na 40.

'Yan wasan Croatia sun samu kwarin gwiwa ne bayan dawowa daga hutun rabin lokaci inda suka kara jefa kwallaye 3 a ragar ta Kamaru

Yanzu dai Kamaru za ta dakata har ranar litinin don karawa da Mai masaukin baki Brazil kafin komawa gida bayan tun a wasanta na farko Mexico ta lashe ta da ci 1 da nema