Kouyate ya koma West Ham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kouyate ya halarci gasar Olympics ta 2012

West Ham ta kammala cinikin dan wasan Senegal Cheikhou Kouyate.

Dan wasan mai shekaru 24 ya taho ne daga zakarun Belgium Anderlecht inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekaru hudu kan kudin da ba a bayyana ba.

"West Ham ta bani damar taka leda a gasar Premier, ina matukar farin ciki," kamar yadda ya shaida wa gidan talabijin na West Ham.

Kouyate na cikin tawagar Senegal a gasar Olympic ta London 2012 , inda ya buga wasan da suka ta shi 1-1 da Burtaniya a filin wasa na Old Trafford.

Karin bayani