Chile ta karya alkadarin Spain

Hakkin mallakar hoto Getty

Chile ta karya lagon Spain a fagen kwallon kafa a duniya bayan ta fitar da ita daga gasar cin kofin duniya a wani wasa mai kayatarwa.

Mai kare kambun ta yi burin zama kasa ta farko da za ta maida kofi gida tun bayan Brazil a 1962, sai dai kash, hakarta ta gaza tun lokacin da Holland ta lallasa ta da ci 5 da 1 wasanta na farko.

Kwallayen da Eduardo Vargas da Charles Aranguiz suka jefa tun kafin tafiya hutun rabin lokaci ne suka bata wa Spain ruwa, inda ta kasa katabus a yunkuri farkewa.

Spain ta zama kasa ta biyar a matsayinta na mai kare kambu da ta gaza tsallake zagayen rukuni a gasar cin kofin duniya a tarihi.

Yanzu dai Spain za ta dakata don yin karawar da-ita-da-babu-duk-daya da Australia a ranar litinin mai zuwa, yayin da za a san wadda za ta kasance ta daya a rukunin B bayan kammala karawa tsakanin Chile da Holland.