'Babu matsala in sauya wuri da Rooney'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Raheem Sterling ya haskaka a wasan Ingila da Italiya

Raheem Sterling ya ce baida matsala ya canja gurbin wasansa da Wayne Rooney, idan hakan zai taimakawa Ingila a gasar cin kofin duniya.

Sterling mai shekaru 19, ya buga wasan farko a kusada Daniel Sturridge amma kuma Ingila ta sha kashi da ci biyu da daya.

A wasan dai matashin dan kwallon ya haskaka kuma kowa ya yabe shi.

Rooney kuwa a bangaren hagu ya buga amma kuma bai taka rawar gani ba sosai.

Sterling ya ce " Bani da matsala in buga duk inda manaja ya sani in buga".

Tsaffin 'yan wasan Ingila Alan Shearer da Rio Ferdinand sun bukaci kocin kasar Roy Hodgson ya saka Rooney a tsakiya don kasar ta taka rawar gani.

Karin bayani