"Yan Super Eagles na iya jima'i da matansu"

'Yan wasan Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Najeriya za ta yi wasanta na gaba ne a rukunin F da kasar Bosnia a Curutiba.

'Yan wasan Super Eagles na Nigeria da ke gasar kofin duniya a Brazil na iya saduwa da iyalansu, amma ban da karuwai a lokacin gasar.

Hakan ya sha bambam da wasu kasashe da suka haramtawa 'yan wasansu yin jima'i a lokacin gasar, kasashen da suka hada da Rasha da Bosnia Herzegovina da Chile da kuma Mexico.

Sai dai wasu kasashe da ke halartar gasar sun ba 'yan wasansu damar saduwa da iyalansu ko kuma 'yan matansu.

Wadannan kasashen su ne Jamus da Spain da Amurka da Australia da Italiya da Holland da Switzerland da Uruguay da kuma Ingila.

Wasu masana kiwon lafiya na ganin yin jima'i zai taimaka wa 'yan wasa, amma wasu masu horas da 'yan wasa ba su amince da hakan ba.

To amma kuma ba a san matsayin sauran kasashen da ke halartar gasar ba kan wannan mataki.