Za a bincika fada tsakanin 'yan Kamaru

Kamaru Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rashin nasarar ya sa an yi waje da Kamaru daga gasar

Kociyan Kamaru Volker Finke ya ce zai bincika dalilin da ya sa Assou-Ekotto ya yiwa abokin wasansa Benjamin Moukandjo karo-da-ka a lokacin da suka sha kashi 4-0 a hannun Croatia.

'Yan wasan biyu suna musayar kalamai ne ana daf da za a tashi wasan lokacin da Assou-Ekotto ya tunkuyi dan uwan na sa.

"Ban taba tsammanin haka ba. Zan bincika ainahin abinda ya faru, me ya sanya wadan nan 'yan wasa yin fada," a cewar Finke.

"Na yi takaicin ganin hakan. Ba shi ne irin martaba da kimar Kamaru da nake son tallata wa ba."

Rikicin ya ci gaba har bayan da 'yan wasan ke ficewa daga fili, kafin Samuel Eto'o wanda ke fama da rauni ya shiga tsakani.

Karin bayani