Colombia ta doke Ivory Coast 2 da 1

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption James Rodriguez ne ya ci wa Colombia kwallon farko

Colombia na kan hanyar ta zuwa zagaye na gaba a gasar cin kofin duniya, bayan ta doke Ivory Coast da ci biyu da daya wasan da suka fafata na rukunin C.

James Rodriguez ne ya soma shigar Colombia gaba a wasan sannan kuma Juan Qunitero ya ci wa kasar kwallo ta biyu.

Gervinho ya farkewa Ivory Coast kwallo daya amma kuma hakan bai sa kasar ta samu nasara ba.

'Yan wasan Ivory Coast sun kai hare-hare amma kuma suka kasa cin Colombia.

A yanzu dai Ivory Coast na bukatar nasara a kan Girka a wasanta na gaba, domin tsallakewa zuwa zagaye na gaba.

Karin bayani